Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, Ayatullah Sayyid Hashim Husaini Bushahri, a cikin hudubobinsa na Sallar Juma’a a birnin Qum, ya yi ishara da dimbin jama’ar da suka halarci jana’izar Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali, inda ya bayyana wannan halarta a matsayin alamar kauna, biyayya da kuma riko da Wilaya daga al’ummomin Iran da Iraki.
Ya bayyana cewa, jama’a sun nuna a cikin kwanaki da dararen da suka gabata cewa ba za su ja da baya ba wajen fuskantar makirce-makirce da shirye-shiryen abokan gaba, kuma ba za su bari makiya su sami damar kutsawa ko cin gajiyar halin da ake ciki ba.
Limamin Juma’ar Qum, yana magana kan manufofin Amurka da yadda kasar ke karya alkawuranta, ya ce: "Wasu mutane a cikin kasar sun yi tunanin cewa tattaunawa da Amurka za ta iya magance matsaloli, amma makiya sun kai wa Iran hari hatta a lokacin da ake cikin tattaunawar, tare da karya alkawura da yarjejeniyoyin da suka dauka."
Mataimakin shugaban Majalisar Kwararrun Jagoranci ya jaddada cewa: "Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta fara yaki, amma ba za ta ja da baya ba idan aka tilasta mata yaki." Ya ce al’ummar Iran za su kare kasarsu da manufofinsu da cikakken karfi.
Ayatullah Husaini Bushahri ya bayyana rushewar girman kai da tasirin Amurka a matsayin sakamakon karfin Jamhuriyar Musulunci, iyawar rundunonin tsaro da kuma tsayin dakan al’ummar Iran, yana mai cewa abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun nuna cewa lissafin siyasa da na soja na makiya ya rushe.
Ya kuma yi ishara da muhimmancin Mashigar Hormuz, inda ya ce: "A yau, Mashigar Hormuz ta zama babban abin tsoro ga abokan gaba, kuma makiya da kansu sun amince cewa rufe wannan muhimmiyar hanya na iya haifar musu da manyan matsaloli."
Limamin Juma’ar Qum ya yi gaisuwa ga Mujahidan da al’ummar Yemen, yana mai cewa: "Kamar yadda Mashigar Hormuz take da muhimmiyar rawa, haka ma Babul Mandab ta zama daya daga cikin muhimman wurare a cikin sabbin ma’aunin siyasar yankin."
Abubuwa Takwas da Ke Jawo Rashin Nasarar Mutum da Al’umma
A wani bangare na jawabinsa, Ayatullah Husaini Bushahri ya yi bayani kan muhimmancin tsoron Allah da hakuri, inda ya ce mutum yana bukatar hakuri domin ya tsaya kan taƙawa, ya jure matsaloli, ya nisanci abubuwan da ba su dace ba da kuma zunubai. Amma wannan hakuri, ya ce, ya fi sauki fiye da hakurin da mutum zai yi wajen fuskantar azabar Allah.
Ya yi ishara da maganar Amirul Muminin Imam Ali (A.S), inda yake cewa:
«فَإِنَّ الصَّبْرَ عَلَى التَّقْوَى أَهْوَنُ مِنَ الصَّبْرِ عَلَى عَذَابِ اللَّهِ»
Ya kuma bayyana abubuwa takwas masu muhimmanci da ke jawo rashin nasarar mutum da al’umma, wadanda suka hada da: sabani da rarrabuwar kawuna, kutsawar masu rashin lafiya a zukata, gafala, rashin lura da sakamakon aiki, gudun sadaukarwa, saba wa Jagoran al’umma, kasancewar mutane masu cin amana, da kuma yada jita-jita.
Shugaban Kungiyar Malaman Makarantar Addini ta Qum ya jaddada cewa kiyaye hadin kai da dunkulewar al’umma, farkawa da taka-tsantsan wajen fuskantar makircin makiya, da kuma guje wa fito da raunanan bangarori a fili a lokacin da makiya ke jiran damar cin gajiyarsu, suna daga cikin muhimman abubuwan da al’umma ke bukata a yau.
A karshen jawabinsa, ya yi ishara da ayar Alkur’ani mai girma:
«لَقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ لِمَنْ كَانَ يَرْجُو اللَّهَ وَالْيَوْمَ الْآخِرَ»
Ya jaddada cewa Juyin Juya Halin Musulunci ya samo asali ne daga sakon Manzon Allah (S), Ghadir da kuma koyarwar Alkur’ani da Ahlulbaiti (A.S), kuma ci gaba da dorewarsa yana da alaka da riko da wadannan koyarwa na Ubangiji.
Ra'ayinka